Dan takarar gwamna karkashin jam'iyyar hamayya ta PDP a jahar Pilato, Jeremiah Useni wanda bai yi nasara a zaben da aka kamala ba, ya ce zai garzaya kotu.
J.T. Useni ya yi barazanar zuwa kotun ne bayan da hukumar zabe ta bayyana gwamna mai ci, Simon Lalong a matsayin wanda ya lashe zaben.
Jihar Pilato na daya daga cikin jihohin da a sake zabe a Najeriyar.
A taron manema labarai da ya kira, Jeremiah Useni ya ce suna kan tattara bayanan da za su gabatar a gaban kotun da ke sauraron kararrakin zabe don kwatar 'yancinsu.
Sai dai Lalong wanda ya lashe zaben karo na biyu karkashin jam'iyya APC, ya yi kira ne ga wadanda suka fadi zaben da su zo su hada hannu don gina jahar ta Pilato.
A halin da ake ciki kuma, a makwabciyar jahar ta Pilato, hukumar zabe ta ayyana Samuel Ortom na PDP a matsayin wanda ya lashe zaben jahar Binuwai.
Saurari cikakken rahoton Zainab Babaji daga Jos: