'Yan Majalisun Amurka na jam’iyyar Democrat sun yi Allah wadai da sanarwar da shugaban Amurka Donald Trump ya fitar cewa zai dakatar da tallafin hukumar WHO, dangane da imanin da ya yi na cewa hukumar ta gaza daukar mataki akan China kan tashin hankalin da Coronavirus ta haddasa.
“Wannan hukunci ne mai hatsari, baya bisa doka kuma za a gaggauta kalubalantarsa,” abin da Kakakin Majalisar Wakilan Amurka Nancy Pelosi ta fada kenan a wata sanarwa.
Pelosi da sauran ‘yan jam’iyyar Democrat, sun yi gargadin cewa ‘kin bayar da tallafi ga hukumar da ke karkashin Majalisar Dinkin Duniya, wadda ke da alhakin kula da lafiya a duniya, zai gurgunta hadin kan al'ummar duniya wajen yaki da wannan annoba ta duniya.
Trump na zargin WHO da jan kafa wajen tabbatar da cewa annobar mai girma ce, da kuma, abin da ya kira, "yada labaran rufa-rufa a madadin China" game da cutar.
Facebook Forum