Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za’a Kawo Karshen Rikicin Kasuwanci Tsakanin Nigeria Da Ghana


Zauren taron kungiyar ECOWAS/CEDEAO a Ghana (Facebook/ECOWAS/CEDEAO)
Zauren taron kungiyar ECOWAS/CEDEAO a Ghana (Facebook/ECOWAS/CEDEAO)

Watanni shida bayan rahoton cibiyar bincike ta kasa-da-kasa, mahukunta a Najeriya da kasar Ghana za su kafa wata doka ta musamman da za ta kawo karshen takaddamar kasuwanci dake tsakanin kasashen biyu da ke zama kawaye a cikin yankin Afirka ta yamma.

An dade ana kai ruwa rana da nufin magance rikice-rikicen kasuwanci da aka kwashe kusan shekaru goma ana yi tsakanin Najeriya da Ghana, lamarin ya yi sanadiyar rufe shagunan ‘yan kasuwar Najeriya a Ghana.

Gwamnatocin kasashen biyu sun rattaba hannu a yarjejeniyar kafa wata doka ta mussaman wacce za ta saukaka kasuwanci da magance rikicin cinikayya da ya dabaibaye kasashen biyu.

Batun hakan ya fito ne ta bakin shugabannin majalisun wakilai na kasashen biyu; Femi Gbajabiamila na Najeriya da Alban Sumana Bagbin na kasar Ghana, a wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja bayan wata ganawar sirri da suka yi.

A cewar Bagbin na kasar Ghana, tuni aka cimma matsaya ta hanyar bullo da wata dabara da za ta hana sake aukuwar rikice-rikice tsakanin ’yan kasuwar kasashen biyu.

Ya ce yanzu haka an kafa wani kwamiti na musamman da ya kumshi zababbun 'yan majalisar wakilai daga kasashen biyu, wadanda za su hada hannu don karfafa dokar da kuma inganta huldar kasuwanci da kawance tsakanin kasar Ghana da Najeriya.

Haka kuma ya ce ana sa ran wakilan kwamitin daga Najeriya za su ziyarci kasar Ghana mako mai zuwa domin soma aiki.

Kasashen biyu dai sun kwashe shekaru da dama suna jayayya kan wata doka da cibiyar bunkasa hannayen jari ta kasar Ghana ta kafa wacce ta kunshi biyan haraji na Dala Miliyan daya ko gabatar da wata kaddara da ta kai adadin kudin, kafin a baiwa wani dan kasuwa daga kasar waje damar kafa kasuwanci da gudanar da harkokin cinikayya a kasar ta Ghana.

Yan kasuwa daga Najeriya dai sun koka akan cewa adadin kudin ya wuce gona da iri.

To sai dai hukumomi a kasar Ghanan sun tsaya kan bakarsu da cewa a matsayinta na kasa mai cikakken iko, tana da' yanci ta kirkira dokoki wanda dole ne duk wani bako ya yi biyayya a gare su.

Idan za’a iya tunawa alamun tabarbarewar dangantaka tsakanin kasashen biyu dai sun faro ne tun bayan matakin mahukuntan tarayyar Najeriyar na rufe iyakokinta da nufin kare kanta bisa ayyukan masu fasakwabri da ma hana shigowa da makamai kasar.

Matakin ya jefa tattali arzikin mutanen kasashen Afirka da dama cikin wani mawuyacin hali, ciki har da kasar ta Ghana.

XS
SM
MD
LG