Kungiyoyin na zargin gwamnati da amfani da ‘yan sanda da sojoji don muzgunawa masu adawa da takaita‘ yancin fadar albarkacin baki da kuma ‘yancin yin taro kamar yadda yake a cikin tsarin mulkin kasar.
Kalaman nasu na zuwa ne bayan an kashe wani dan gwagwarmaya mai yakin kamfen din neman #gyara kasarmu ko kuma # FixTheCountry a turanci. Gangamin na neman ingantaccen shugabanci da gyara yanayin rayuwa.
Zanga-zangar game da kanfen din ya haifar da rikici tare da ‘yan sanda wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane biyu.
'Yan adawa da kungiyoyin farar hula sun yi Allah wadai da mutuwar a matsayin abin da ba za a yarda da shi ba. A halin yanzu, Shugaba Nana Addo ya bayyana jimaminsa tare da neman a gudanar da binciken lamarin. Magoya bayan sa sun ce sukar ba ta da tushe ta kuma kara da cewa 'yan adawar na neman cin nasara a fagen siyasa ne daga wannan yanayi mara dadi.
Mensah Thompson shi ne babban darakta na Alliance for Social Equity and Public Accountability (ASEPA), wata ƙungiyar jama'a. Ya fadawa wakilin Muryar Amurka Peter Clottey cewa ya kamata kasashen duniya su damu da amfani da ‘yan sanda da sojoji ke yi wajen murkushe‘ yan kasar da ke neman kyakyawan shugabanci da gwamnatin tayi masu alkawari.