Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce za ta dakatar da gwajin maganin hydroxychloroquine na jinyar masassarar cizon sauro da kuma hadin magungunan lapinavir/ritonavir na jinyar cutar HIV mai karya garkuwar jiki akan wadanda suka kamu da cutar COVID-19 ake kuma jinyarsu a asibiti, bayan da magungunan suka kasa rage adddin mace-macen da ake samu.
Wannan koma bayan na zuwa ne a yayin da hukumar WHO ta sanar da cewa a karon farko mutum sama da 200,000 suka kamu da cutar coronavirus a rana guda a fadin duniya. An samu mutum 53,213 a Amurka daga jimlar mutum 212,326 da suka kamu da cutar a ranar Juma’a 3 ga watan Yuli a cewar hukumar.
Hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce wannan matakin, wanda kwamitin da ke sa ido kan gwajin magunguna na kasa da kasa ya bada shawara a dauka, ba zai shafi sauran bincike-binciken da ake yi a bangarorin da ake amfani da magungunan kan marasa lafiyar da ba a kwantar a asibiti ba ko kuma a matsayin maganin kariya.
Facebook Forum