A wannan makon ne Shugabar hukumar kare hakkin bil adama ta Majalisar Dinkin Duniya Michelle Bachelet da kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch suka gabatar da wannan zargi, in ji Gwamnatin mulkin sojan Mali a cikin wata sanarwa da ta buga a ranar Alhamis.
Kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch ta fada a ranar Talata cewa sojojin Mali ne suka kashe akalla fararen hula 71 tun farkon watan Disamba.
Gwamnatin mulkin sojan Mali ta gudanar da juyin mulki sau biyu tun daga watan Agustan shekarar 2020. A cikin sanarwar ta bayyana abin da ta kira yada-yadan labarai "wani dabara ce da aka tsara domin tada zaune tsaye a fagen siyasar kasar, da ruguza al'ummar Mali da kuma bata sunan sojojin Mali."
Kafofin yada labaran biyun sun ci gaba da aiki a Mali a safiyar Alhamis.
Hukumar mulkin sojan ba ta bayar da cikakken bayani kan tsarin ba, ko kuma ta fadi lokacin da za a dakatar da watsa shirye-shirye. A baya, kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya ruwaito cewa dakatarwar ta fara aiki.
France Medias Monde, kamfanin mallakan gwamnati wanda France 24 da RFI ke cikin rassansa, bai amsa bukatar jin ta bakinsa ba.
~ REUTERS