Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za A Baiwa 'Yan Kasashen Waje Lambar Zama Najeriya Ta Wucin Gadi


Akwai bukatar kowane jami'in kasar ketare ya samu lambar zama dan kasa ta wucin gadi a Najeriya.

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ce samar da lambar shaidar zama dan kasa ta zama tilas ga jami'an diflomasiyyar Kasashen waje, wadanda za su ci gaba da zama a kasar na tsawon shekaru biyu ko sama da haka.

A lokacin da ya ke yi wa Muryar Amurka bayani akan matakin, babban Darekta a Hukumar Bada Katin zama dan kasa, Injiniya Aliyu Aziz, ya ce a bisa umurnin Ministan Sadarwa Dr. Isa Ali Pantami, ne aka bude wannan wuri, kuma cibiyar yin rajistar za ta yi wa mambobin diflomasiyyar jagora, sannan za a kula da su ne ta Ma'aikatar Sadarwa ta Tarayya tare da hadin gwiwa da Hukumar bada katin Dan Kasa.

Injiniya Aziz, ya ce akwai katin NIN na wucin gadi wanda za a hada shi da bayanan da ke jikin fasfo din jami'i, wanda ya ke aiki na wucin gadi a kasa.

Wannan matakin ya dauki hankalin tsohon Jakadan Najeriya Suleiman Dahiru, inda ya ce wannan mataki ne mai kyau, tunda an ce kowa da kowa ya yi rajistan layin wayar sa da lambar NIN dinsa, kuma wadanan mutane suna tareda mu a nan gida Najeriya.

Mai nazari a al'amuran yau da kullum Imrana Wada Nas, ya bayyana ra'ayinsa a game da matakin, da mahukunta suka dauka yana cewa, Idan za a dore da yin haka, to lallai nan da dan lokaci kadan za a gane miyagu masu amfani da wayar hannu, ko dandalin sada zumunta wajen tafka ta'addanci da wulakanta dokokin kasa, ana fakewa da guzuma ana harbin karsana.

Wanan cibiya da aka bude ta musamman ce domin jami'an diflomasiya, kuma zata fara aiki daga ranar Talata 19 ga wannan watan na Janairu.

Ga rahoton Medina Dauda a cikin sauti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:29 0:00

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG