Suka ce tilas ne gwamnatin ta kasar ta baiwa rundunar sojojin yankin goyon bayan da take bukata domin gudanar da ayyukan ta. Domin nan bada jimawa bane ake sa ran sojojin su bayyana a kasar ta Sudan ta Kudu.
Daya daga cikin ire-ire wadannan mutanen da suke wannan kiran ko sun hada da Farfesa Jacob Chol, wanda yake shine shugaban babban kwalejin kimiyyar siyasa ta jamiaar dake babban birnin kasar wato Juba.
Yace wannan yukurin na kungiyar abin marawa baya ne musammam na ganin cewa zata aiko da sojojin ta a kasar domin tabbatar da samar da zaman lafiya a Sudan ta Kudu.
Chol yace kar alkawarin ya zamo na fatar baki kawai, amma ya zamo a aikace, yace muddin ba a gaggauta daukar matakin daya dace ba to duk wata yarjejeniyar da aka cimmawa zai zamo shirme.
Shehin malamin yace abu mafi muhimmaci shine a tabbatar an kaddamar da wannan kudirrin yanzu-yanzun nan, musamam ma a tabbatar cewa shugabannin hafsoshin kasashen kungiyar ta raya kasashen gabashin Africa sun gana da takwaran su na kasar Sudan ta Kudu akan yadda zasu gudanar da wannan aiki, musammam akan batun da yashafi gudun mowar kudi da kuma sauran ayyuka.