Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yunkurin Rage Sojojin Kuntunbalan Amurka A Nahiyar Afirka Ya Jawo Sabanin Ra'ayi Tsakanin Masana Tsaro


Sakataren Tsaron Amurka Janar Jim Mattis
Sakataren Tsaron Amurka Janar Jim Mattis

Jaridar New York Times ta fara ruwaito labarin yunkurin rage sojojin kuntunbalan Amurka a nahiyar Afirka kuma kodayake ma'aikatar tsaron Amurka, Pentagon ta amince da batun har yanzu ba'a yanke shawara ta karshe ba

Shirye shiryen da ake yi na rage aiyukan sojojin kuntunbalan Amurka da aka tura nahiyar Afrika yana jawo sabanin ra’ayi tsakanin masana harkokin sojan Amurka.

Jaridar New York Times da ake bugawa a birnin New York ta bada labarin shirin da aka gabatar a wannan makon daya tanadi rage yawan sojojin kuntunbalan Amurka daga kimamin dubu daya da dari biyu zuwa dari bakwai cikin shekaru uku.

Jami’ai sun baiyana wa Muryar Amura cewa kodayake jami’an ma’aikatar tsaron Amurka da ake cewa Pentagon sun amince da batun rage yawan sojojin to amma har yanzu ba’a yanke shawara ta karshe akan wannan batu ko mataki ba.

Wannan shawarar rage yawan sojojin da aka gabatar ya biyo bayan nazarin wani al’amari daya faru a watan Oktoba lokacin da aka yiwa wasu sojojin Amurka guda hudu kwantar bauna aka kashe su a jamhuriyar Niger.

Binciken da ma’aikatar tsaron Amurka ta gudanar akan wannan al’amari ya gano kura kurai da dama ta bangaren sojojin. Wannan al’amari yasa wasu wakilan Majalisar dkokin Amurka bukatar a rage yawan sojojin Amurka a Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG