Kamfanin dillancin labarai na Najeriya – NAN, ya ruwaito mai Magana da yawun hukumar gidan yari a jihar Abubakar Adamu, yana cewa lamarin ya auku ne a jiya Juma’a, sakamakon wani jami’i da ya shiga da wasu kayayyaki ga fursunoni a haramce.
“An sami hatsaniya ne sakamakon halayyar wani jami’in hukumar gidajen yari, da ke shigar da wayyoyin salula da miyagun kwayoyi wa fursunoni da ke gidan yarin,” in ji Abubakar Adamu.
Ya ce fada ne ya soma tashi tsakanin fursunonin da aka shigarwa da kayayyakin a haramce, da kuma jami’an da ke kokarin hana aukuwar ayukan da suka saba ka’ida a gidan yarin.
Abubakar ya kara cewa “an yi sa’ar ganin jami’in dumu-dumu yana aikata wannan haramtaccen aikin aka kuma kama shi, abin da ke nan ya bakanta ran fursunonin da aka shigar wa da kayayyakin, suka ta da bore har suka fasa dakunan ajiye kayayyaki, suka kwashe shebura da digogi da sauransu.”
Daga nan ne fa fusatattun fursunonin suka soma rera wakoki da take, inda suka ci gaba da farfasa gine-gine da kayayyaki a cikin gidan yarin, lamarin da kuma ya tilastawa jami’an hukumar soma harbi a iska domin razanasu, wanda kuma yayi sanadiyyar fursunoni 5 da jami’ai 2 suka ji rauni, a cewar kamfanin dillancin labaran na NAN.
To sai dai Abubakar Adamu ya ce tuni da aka sami shawo kan matsalar, yayin da kuma dukkan fursunoni suka koma dakunansu.
Rahotanni sun bayyana cewa an tsaurara matakan tsaro tare kuma da takaita zirga-zirgar ababen hawa a kewayen gidan yarin, kana kuma aka sanya shingaye akan dukkan titunan da ke zuwa gidan yarin.