Mukaddashin babban kwanturola-Janar na Hukumar kula da gaggawa ta Najeriya NCoS, John Mrabure, shi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa.
A cewar sanarwar, Mrabure ya bayar da umarnin a gudanar da cikakken bincike a kan lamarin.
Wani mai magana da yawun kungiyar ‘yan asalin yankin Biafra masu neman ballewa ya shaida wa kamfanin dillacin labarai na AFP cewa, zargin da ake yi kungiyar cewa ita ke da alhakin harin ba shi da kanshin gaskiya.
Karin bayani akan: Boko Haram, Owerri, John Mrabure, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.
Jihar Imo ta dade tana a matsayin wurin da kungiyoyin 'yan awaren ke tinkaho da shi, yayin da dangantaka tsakanin gwamnatin tsakiya da' yan asalin kabilar Ibo ta yi tsami.
Da yake maida martani dangane da lamarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya umarci dukkanin hukumomin tsaro da na leken asiri su tabbatar da kame tare da hukunta duk wadanda suka kai munanan hare-hare a shalkwatar rundunar ‘yan sanda ta jihar Imo da kuma gidan yarin na Owerri da safiyar Litinin.