Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

YEMEN: Dakarun Hadakar Kasashen Larabawa Sun Kwace Filin Saukar Jiragen Sama Daga Mayakan Houthi


Ministan harkokin wajen Saudiyya Minister Adel al-Jubeir
Ministan harkokin wajen Saudiyya Minister Adel al-Jubeir

Nasarar kwato filin saukar jiragen sama na Hodeida zata ba hadakar dakarun Larabawa dake fafatawa da mayakan Houthi dake samun goyon bayan Iran damar cafke tashar jiragen ruwa dake da mahimmanci.

Dakarun hadaka na kasashen Larabawa, sun karbe filin tashin jiragen saman Hodeida daga hannun mayakan Houthi da ke samun goyon bayan Iran.

Wannan babbar nasara ce a yunkurin kwato birnin mai tashar jiragen ruwa, bayan da aka kwashe mako guda ana gwabza fadan da ya watsu zuwa yankunan fararen hula.

Kwamandan hadakar dakarun kasashen Larabawa, Abdul Salamm Al Shehi ne ya fitar da sanarwar kwato filin jirgin a jiya Laraba, a wani hoton bidiyo da Hadaddiyar Daular Larabawa ta wallafa a shafin kamfanin dillancin labaranta na WAM.

Wannan yunkuri na kokarin kwato wannan birni, ya haifar da fargaba kan yiwuwar jefa al’umar yankin cikin mummunan yanayi, saboda nan ne babbar hanyar shigar da kayayyaki ga ‘yan Houthi, kuma madogara wajen samun ababan rayuwa ga miliyoyin ‘yan kasar ta Yemen.

A shekarar 2015, dakarun da Saudiyya ke jagoranta suka shiga yakin basasan na Yemen, domin taimakawa gwamnati wajen dakile ikon da ‘ya Houthi suka samu na karbe muhimman wurare a kasar, su kuma maido da gwamnatin da kasashen duniya suka amince da ita kan karagar mulki.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG