A yau Talata shugaban Amurka Donald Trump ya isa kasar Koriya ta Kudu, a zaman wani bangare na ziyara da yake yi a yankin wanda batun shirin makaman Koriya ta Arewa ya mamaye ta.
A yayin wannan ziyara ta kwanaki biyu, ana sa ran Trump zai tabbatar da kudurin Amurka na kare kawayenta daga barazanar Koriya ta Arewa, a yayinda ake fama da karin zaman ‘dar ‘dara zirin Koriyar.
A farkon makon nan a Japan, Trump da Prime Ministan Japan Shinzo Abe, suka amince da cewa har yanzu akwai sauran zabin da za’a iya amfanin da su, idan aka zo batun Koriya ta Arewa.
A cewar Shinzo Abe jiya Litinin, a wani taron manema labarai da yayi da Trump, yace, “babu wani amfanin zaman tattaunawa da Koriya ta Arewa” kuma lokaci yayi da ya kamata a matsawa Pyongyang lamba sosai.
Bayan tarurrukan da suka yi a ranar ta biyu, Abe da Trump, sun tabbatar da cewa batun Koriya ta Arewa ya kanainaiye tattaunawarsu.
Facebook Forum