Kamar ko'ina a fadin duniya, jamhuriyar Niger ta tuna da ranar yawon bude ido, sai dai wannan fannin na huskantar koma baya a kasar, Hakan ya faru ne a sanadiyar tawayen da Abzinawa su kayi a ‘yan shekarun da suka gabata da kuma rashin tsaro dake samun asali daga yake - yaken da a keyi a kasashen Libiya da Mali na ‘yan tsananin Islama.
Kasancewar ‘yan yawon bude idon dake zuwa Niger na sha'awar ziyarar arewacin kasar mai cike da tarihi amma kuma nan ne aka fi fama da rikici saboda haka suka kaucewa kawo yawon kasar.
Ahmed Botto minstan yawon bude ido y ace aiki ne da yake da mahimmanci ga kasarsu saboda ko wadanda bas a aiki cikin ka’ida suna samun anfani.
Haruna Baba shugaban ma'aikatar yawon bude ido ta jahar Agadez ta Niger, yace a can baya da turawa ke tururuwa zuwa arewacin kasar ana samun alheri sosai. Y ace ko kudin sefa da suke kashewa ta Faransa ce wadda turawa ke kawowa lokacin yawon bude ido. Masu aikin hannu ma suna samun kudi ainun. Labarin da ake ba turawan akan yanayin tsaro ya kawo masu miskila
Shima Mahamadu wani makeri da a can baya ke samun kudade sosai daga hannun turawa ‘yan yawon bude dake ziyartar Niger, ya ce a halin yanzu ba bu wata damawa daga hannun yan yawon bude idon saboda sun ragu
Koma bayan sha'anin shigar kudade wa Niger ba karamar hasara ce ba sanadiyar karancin ‘yan yawon bude ido dake shakkar tsaron lafiyar su ganin cewa kasshen dake makwaftaka da Niger sun a fama da ayyukan ta’addanci.
A saurari rahoton Haruna Mamman Bako
Facebook Forum