Wadanda suka sauya shekar sun hada da Malam Nuhu Ribadu wanda shi yayi wa PDP takara a zaben da ya gabata, sai kuma wani dan takarar gwamna na jam’iyar SDP, Engr Markus Gundiri da kuma tsohon gwamnan jihohin Borno da Lagos, Birgediya Janar Buba Marwa wanda tun farko da suka kafa jam’iyar APC.
To sai dai kuma tun farko da yake karbar wadanda suka koma, shugaban riko na jam’iyar a jihar Hon. Ibrahim Bilal, gargadi yayi da cewa dole a hada kai.
To amma kuma a jawabansu Malam Nuhu Ribadu da Engr Markus Gundirir duk sun wayar da kai. Kawo yanzu tuni wasu ke zargin cewa da wata manufa suka koma jam'iyyar, batun da Engr Markus Gundiri ke musantawa.
Ko a makon jiya sai da wani hadimin gwamna, kuma shugaban ma’aikata na gidan gwamnatin jihar Alh,Abdulrahman Abba Jimeta, ya fito yayi gargadin cewa wasu kusoshin jam’iyar APC,na neman kawo wasu jam’iyar don dagula tafiyar gwamnatin jihar.
Koma da menene dai yanzu an zura ido aga yadda wannan lamari na jam’iyar APC, a Adamawa zai kaya, ganin cewa jam’iyar ta raba gida biyu wato a tsakanin magoya bayan gwamnan jihar dake dasawa da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, da kuma 'yan bangaren su tsohon gwamnan jihar Murtala Nyako dake tare dasu sakataren gwamnatin Najeriya Babachur David Lawal dasu ministan Abuja!
Ga rahoton Ibrahim Abdul'Aziz daga Abuja.