Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Ban Ki-moon ke ziyarar Sudan ta Kudu


Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon
Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon

Yau ne sakataren Majalisar Dinkin Duniya ko MDD a takaice Ban-ki moon ya ziyarci Juba fadar gwamnatin Sudan Ta Kudu domin ya gana da shugaba Salva Kiir, kana ya ziyarci sansanin yan gudun hijira dake karkashin kulawar MDD wadanda yakin kasar ya shafa.

Ziyarar ta Ban Ki-moon tazo dai-dai da lokacin da sassan biyu da ke fada da juna suka dauri aniyar samar da gwamnatin hadin kan kasa wadda tana cikin yarjejeniyar da aka cimma a cikin watan Agustan bara.

Hukumar kula da tantancewa ta kasar ta Sudan ta Kudu ta bayyana a ranar Talata cewa yarjejeniyar da aka cimma ta amince da sojojin da ke goyon bayan Riek Marchar har su 1,370 su shiga babban birnin kasar, wannan ko duka yana cikin yunkurin na shi Marcher ya shiga cikin gwamnatin ta hadin kan kasa ne.

Haka kuma ana sa ran a samu karin jamian tsaro da zasu shiga cikin gwamnatin ta hadin kan kasa da zaran an samar da gwamnatin.

An cimma matsaya ne dai bayan an kwashe shekaru biyu ana tafka yaki tsakanin Riek Marchar da shugaba Salva Kiir wandasai a cikin watan Agusta ne aka cimma matsaya akan samar da gwwamnatin hadin kan kasa, wadda zata ta kwashe watanni 30 tana mulki kafin a gudanar da zabe a kasar.

Yanzu haka Shugaba Kiir ya sake nada Merchar a matsayin mataimakin sa a cikin gwamnatin sabuwa da ake shirin kafawa

XS
SM
MD
LG