Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau asabar kungiyar NATO ta zafafa hare harenta a Libya


Mayakan yan tawayen Libya suke murna bayan sun mamaye Zirtan.
Mayakan yan tawayen Libya suke murna bayan sun mamaye Zirtan.

Yau asabar kungiyar kawancen tsaro ta NATO ta zafafa hare haren da take kaiwa Libya, wanda a karon faro ta tura jiragen saman yaki masu saukar angulu, suka yi shawagin kasa kasa sosai somin su kaiwa sansanonin sojan Gaddafi hare hare.

Sakataren tsaron Ingila William Hague ya isa Libya domin ganawa da masu hamaiya a birnin Benghazi. Sakataren na tsaron Ingila ya isa Libya ne a yayinda a yau asabar kungiyar kawancen tsaro ta NATO ta zafafa hare haren da take kaiwa Libya, wanda a karon faro ta tura jiragen saman yaki masu saukar angulu, suka yi shawagi kasa kasa sosai domin su kaiwa sansanonin sojan Gaddafi hare hare.

Kungiyar NATO tace jiragen sama yakin Britaniya samfurin Apache dana kasar Faransa samfurin Tiger da kuma samfurin Gazelle sune suk kai hare haren. Jami’an soja sunce an lalata wurare ashirin da aka auna cikin harda wani wurin da aka adana na’urar hangen abubuwa da wani wurin bincike na soja. Dukkan wadannan jiragen saman yaki guda uku da suka kai hare haren suna dauke da makamai masu linzami.

Kwamandan sojojin kungiyar NATO a Libya Janaral Charles Bouchard na Canada yace nasarar da aka samu na kai hare haren sun nuna iyakar jiragen yakin masu saukar angulu na kai hare hare ba tare da jikatta farar hula sosai ba. NATO ta kara kaimin hare haren da take kaiwa a Libya ne, a yayinda kuma aka kara kaimin yunkurin diplomasiya na ganin cewa shugabva Gaddafi ya yarda ya ajiye ragamar mulki.

XS
SM
MD
LG