Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar tsaro ta NATO ta kara wa'adin zamanta a Libya


Wani ginin gwamnati da dakarun NATO suka kaiwa hari a Libya
Wani ginin gwamnati da dakarun NATO suka kaiwa hari a Libya

Rundunar sojan Turai ta NATO tace zata kara kwannaki 90 ga zamantan a kasar Libya tunda shugaban kasar Muammar Ghadafi yaki sauka daga karagarsa ta mulki.

Rundunar sojan Turai ta NATO tace zata kara kwannaki casa'in ga zamantan a kasar Libya tunda shugaban kasar Muammar Ghadafi yaki sauka daga karagarsa ta mulki. Babban sakataren NATO, Anders Fogh Rasmussen yace sun dauki matakan tsawaita zaman nasu ne don aikawa Ghadafi sakon cewa ba zasu sassabta matsin lambar ganin ya sauka ba. A da, jadawalin da aka shata na hana zirga-zirgar jiragen Libya a cikin sararin samaniyarta a karshen watan nan na Yuni ya kamata ta kare, to amma yanzu wannan karin lokacin yana nufin ke nan za’a ci gaba da yakin har sai cikin watan Satumba

XS
SM
MD
LG