A Maradin Jumhuriyar Nijer an gudanar da wnanan biki na tunawa da ranar SIDA/Kanjamau ne a makarantar horas da Malaman makaranta ta Bawa Jan Gwarzo.Wakilin Sashen hausa Choibu Mani ya nemi Karin bayani kan matakan da hukumomin lafiya ke dauka domin kauda wannan cuta daga wajen jagoran shirin ganganim taron Dr.Alisu Manu Yaro wanda yake cewa babban burin dake gaban hukumomin jumhuriyar Nijer shine a tabbatar an kai ga kauda wannan cuta ta Kanjamau/Sida daga jumhuriyar Nijer baki dayanta ta ayadda nan ya zuwa shekara ta 2015 ba’a sami koda mutum guda dake dauke da cutar ba a Jumhuriyar Nijer. Kuma wadanda ke dauke da cutar a kokarta tabbatar da samar masu abinchi mai gina jiki tare da basu maganin rage radadin cutar. Daga shekarar 2010 zuwa 2011 an kiyasta cewar akwai wadanda suka kamu da cutar kanjamau 992.
Saurari