Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ko OMS a takaice, ta gabatar da rahoton cewa daga shekarar dubu biyu an samu raguwar mace-mace sanadiyar cutar maleriya ta zazzabin cizon sauro da fiye da kashi 20 cikin dari.
Hukumar Lafiyar ta Duniya, ta ce yawan mace-macen sun ragu daga dubu 985 a shekarar dubu biyu zuwa kimanin dubu 780 a shekarar dubu biyu da 9. Yawancin mace-macen kan shafi yara kanana ne a kasashen Afirka.
A yau talata Hukumar Lafiyar ta Duniya ta gabatar da kididdigar ta, ta baya-bayan nan, a cikin rahoton ta na shekarar dubu biyu da 10 na cutar zazzabin cizon sauro a duniya.
A cikin shekaru goman da su ka shige, adadin masu kamuwa da cutar maleriya ta zazzabin cizon sauro a kowace shekara ya ragu kadan, daga miliyan 233 zuwa miliyan 225.
Rahoton ya danganta raguwar kamuwa da cutar da daukan matakan rigakafi da kuma takaita bannar cutar.
Duk da cewa zazzabin cizon sauro cuta ce mai warkewa kuma wadda ake iya yin rigakafin ta, hukumar Lafiya ta Duniya ta ce a Afirka yaro daya ne ke mutuwa da cutar a cikin dakika 45 daga fitowar rana zuwa faduwar ta, zazzabin cizon sauro ne sanadin mace-macen yara kanana kusan kashi 20 cikin dari a Afirka.