Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Ake Bikin Zagayowar Ranar Kula Da Yawan Al'uma.


kakakin Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon, da tsohon skataren, Kofi Annan.
kakakin Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon, da tsohon skataren, Kofi Annan.

Laraba ce kasa da kasa suka yi bikin tunawa da ranar ‘Yawan al’umma’ a duniya.Batun da aka fi maida hankali wajen yin Magana kansa shine bunkasa hanyoyin kiwon lafiyar jama’a a duniya.

Laraba ce kasa da kasa suka yi bikin tunawa da ranar ‘Yawan al’umma’ a duniya.Batun da aka fi maida hankali wajen yin Magana kansa shine bunkasa hanyoyin kiwon lafiyar jama’a a duniya.

Babban Magatakardar MDD Ban Ki-moon yace bunkasa hanyoyin kion lafiyar masu haihuwa ba karamin zuba jari bane a halin zaman rayuwar Bil Adama. Hakan ne kuma ke kara karfafa ayyukan kiwon laafiyar al’ummar kasa da kasa. Yace ganin yadda yawan al’ummar duniya ke ci gaba da karuwa har nunki uku a kiyasin MDD, za’a sami matan da zasu sami haihuwa kusan miliyan metan da ashirin da biyu a sassa dabam-daban musamman kasashe masu tasowa wadanda kuma keda matsalar kiwon lafiyarsu tun daga daukan ciki har zuwa lokacin haihuwa, balle ayi Maganar tsarin iyali.

Dr. Dhammika Perera, jami’a ce da ta kware wajen bada shawarar ayyukan kiwon lafiyar mata lokacin haihuwa, ta shaidawa Muryar Amurka cewa muhimmin abin bukata a yanzu shine samar da hanyar baiwa mata masu haihuwa tallafin sanin yadda zasu kula da lafiyarsu tun daga daukan ciki har zuwa lokacin haihuwa, sai kuma uwa uba, yadda za‘a kula da jariran bayan haihuwarsu, da samar masu abinchi mai gina jiki.

Matsalar da yanzu tafi addabar kasashe masu tasowa ke nan da tasa jarirai ke yawaita mutuwa. Dr. Perra ta kara da cewa koda yake mafi yawan matan dake fuskantar haihuwa a kasashe masu tasowa sun fi maida hankalinsu ne wajen sanin hanyar bunkasa halin zaman rayuwarsu ta yau da kullum, wato abinchi da sutura, amma gaskiyar maganar itace rage yawan haihuwa da kayyade iyali sune tuwasun yaki da talauchi da fatara.

XS
SM
MD
LG