Yau ake hawan arafa a kasa mai tsarki kuma wakilin Muryar Amurka Nasiru Adamu El-Hikaya ya zanta da Aliyu Mustapha akan abubuwan dake gudana a cigaba da ayyukan hajjin wannan shekarar ta 2017.
Inji Nasiru dubban mutane suka yi kokarin hawan tsaunin Arafa duk da zafin da suka fuskanta. Tsaunin Arafan shi ne wurin da Annabi Muhammad (SAW) ya yi hudubarsa ta karshe. A tsarin aikin hajji ba lallai ba ne sai ,mutane sun hau amma duk da haka mutane sun kasance a kan tsaunin.
Daga Najeriya alhazai dubu sittin da biyar ne suke aikin hajjin bana (65,000). Akwai kuma wadanda suka bi jirgin yawo su dubu goma sha daya (11,000). Kawo yanzu alhazan Najeriya guda bakwai ne suka rasa rayukansu.
Yau an yi zafi ainun saboda zafin ranar ta kai awon digiri 50 na celcius. Akwai wadanda suka taimaka da barbada ruwa ta sama domin rage zafin ranar. Wadanda basu da laima sun dandana kudarsu.
Hadin kan da aka samu daga masu gudanar da ayyukan hajjin daga Najeriya ya banbanta hajjin bana da na shekarun baya. Jami'an Saudiya sun lakadawa wasu alhazan jihar Neja duka lamarin da ya sa gwamnatin Najeriya ta bara har sai da gwamnatin Saudiya din ta bada hakuri. Tun daga lokacin alhazan Najeriya suka samu masalaha.
An kebewa kasashen Afirka wadanda ba larabawa ba ne yanki guda kuma suna nan lafiya. Amma duk alhazan kasashen bakaken Afirka idan an hadasu basu kai na Najeriya yawa ba.
Ga firar Nasiru Adamu El-Hikaya .
Facebook Forum