Babban jami’in Majalisar Dinkin Duniya mai wanzar da zaman lafiya, ya fada jiya laraba cewa, yarjejeniyar da aka cimma ta dakatar da bude wuta a kasar Sudan ta kudu batayi tasiri ba domin kuwa har yanzu kasar na cikin halin zaman dar-dar.
Har yanzu ana zaman tankiya duk ko da yake an cimma matsaya na dakatar da bude wuta wanda shugaban kasar Salvar Kirr ya amince dashi.
Yanzu haka dai ana ci gaba da fada a wadansu sassan kasar kamar yadda Jean-Pierre Lacriox ya shaidawa kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya.
Yace musali a arewacin kasar, sojojin gwamnati sun fatattaki sojojin ‘yan adawa daga wurin da suke da karfi a yammacin gabar kogin NILE,
Sai kuma a gabashi sojojin sun karbe garururuwan dake arewacin Jonglei yayinda kuma a yammaci ana samun fada tsakanin sojojin gwamnati da na ‘yan adawa a yankin Wau, sai kuma a kudanci inda yanzu haka mutane duk sun watse a wadansu garuruwan dake yankin Ekutorial, suka zama kango
Facebook Forum