Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yarjejeniyar Da Aka Cimma A Sudan ta Kudu Ta Wargaje


Tsohon mataimakin shugaban kasa Rick Machar da Shugaban kasar ta Sudan ta Kudu Silva Kiir sun sha hannu yayinda suka rabtaba hannu akan yarjejeniyar da suka cimma makon jiya
Tsohon mataimakin shugaban kasa Rick Machar da Shugaban kasar ta Sudan ta Kudu Silva Kiir sun sha hannu yayinda suka rabtaba hannu akan yarjejeniyar da suka cimma makon jiya

Wata hadakar kungiyar 'yan tawaye a Sudan ta Kudu sun yi watsi da yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma a Uganda tsakanin bangaren shugaban kasa da bangaren tsohon mataimakinsa

'Yan tawaye a Sudan ta kudu sun yi watsi da yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnatin kasar tayi ikirarin cewa duka sassan biyu sun amince dashi. Wannan labarin ya kashe gwuiwar dokin da ake dashi na ganin an kawo karshen yakin basasar kasar na kusan shekaru biyar.

A rahoton da Mohammed Yusuf ya aikowa Muryar Amurka daga Nairobi, ya ce a cikin wata sanarwa da kungiyar 'yan tawayen Sudan da Kudu da ake kira SPLM ta ce hakika an tattauna kan batun daunin iko- amma ba'a cimma matsaya a hukumance akai ba.

Tunda farko wata hadakar 'yan hamayyar kasar data kunshi jam'iyu tara,wacce ake kira South Sudan Opposition Alliance da turanci ta yi watsi da yarjerjeniyar.

Kwaje Lasu, shi ne kakakin hadakar, ya ce

Bamu da hanu a cikin yarjejeniyar. Wannan ya kaucewa amannar da mukayi da damawa da kowa. Bugu da kari, duk shawarwarin da aka yi da sunan daftari kan daunin iko-hakan bai tabo baki daya musabbabin rikicin ba."

Shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir, da shugaban 'yan tawaye Riek Machar sun gudanar da shawarwari ranar Asabar a birnin Entebbe, wani ziri a tafkin Victoria.

Duk da cewa ba'a tsammain a cimma matsaya da zata warware fitinar baki daya, akwai tsammanin a sami zaman lafiya ganin matakai da aka dauka na baya bayan nan.

Sassan biyu da suke gaba da juna, sun amince ranar Jumma'a su janye dakaru daga birane, bayan da aka cimma yarjejeniyar zaman lafiya a karshen watan Yuni.

Facebook Forum

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG