Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

SUDAN TA KUDU: Yarjejeniyar Tsagaita Wuta Ta Ruguje Sa'oi Bayan Fara Aiki


Shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir, da shugaban adawar Riek Machar
Shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir, da shugaban adawar Riek Machar

Gwamnatin Sudan ta Kudu da 'yan tawaye suna tsirawa juna hannu kan rugujewar yarjejeniyar tsagaita wuta cikin 'yan sa'oi da fara aiwatar da ita.

Yarjejeniyar tsagaita wutar da shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir da ‘yan tawaye suka sanyawa hannu ta ruguje yau asabar, ‘yan sa’oi bayan fara aiwatar da ita, yayinda dukan bangarorin suke zargin juna da fara kai hare hare a kasar.

Kakakin ‘yan tawaye Lam Paul Gabriel ya zargi dakarun gwamnati da kai hari a wuraren ‘yan tawaye dake bayan garin Wau arewa maso yammacin Sudan, cikin sa’oi shida da fara aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wutar.

A nashi bayanin, Kakakin gwamnati Ateny Wek Ateny ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Associated Press cewa, kungiyar hamayya ce ta kai harin, yace kungiyar bata da shugabannin kwarai, babu wanda yake masu jagoranci.

Kiir da Reik Machar, tsohon mataimakin Kiir sun sa hannu a yarjejeniyar stagaita wuta ranar Laraba bayan tattaunawar gaba da gaba a Khartoum babban birnin kasar Sudan.

Yarjejeniyar ta kuma yi kira da a bude hanyoyin gudanar da ayyukan jinkai, a saki fursunoni a kuma janye sojoji, bisa ga cewar kamfanin dillancin labarai na kasar Sudan SUNA.

Kamfanin dillancin labaran ya kuma laburta cewa, kungiyar hadin kan kasashen nahiyar Afrika da kuma kungiyar hadin kan kasashen gabashin Afrika zasu sa ido kan yarjejeniyar tsagaita wutar. .

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG