Wani rahoton Asusun tallafawa yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, ya ce ba a mayar da hankali kan yadda za a kare yara daga annobar coronavirus da ta addabi duniya.
UNICEF ta ce duk da cewa cutar ta COVID-19 ta fi kama masu yawan shekaru, akwai yiwuwar ta yi mummunan tasiri akan yara a duk fadin duniya.
Asusun ya kuma nuna cewa, duk da cewa matakan da ake dauka na dakile yaduwar cutar na da muhimmanci amma ya ce za su iya shafar rayuwar yara.
Laurence Chandy, shi ne darektan ofishin tsare-tsare a hukumar ta UNICEF ya kuma ce kashi 60 na adadin yara a duniya na zaune ne a kasashen da aka saka dokar hana fita, matakin da ya kai ga rufe makarantu.
Rahoton ya ambato cewa akwai yara sama da miliyan 360 a kasashen 143 da suka dogara da abincin da makarantu ke ba su.
Facebook Forum