Hukumar kula da lafiya ta duniya ta fitar da wannan bayani ne a taron data gudanar a Geneva a karshen watan oktoban wannan shekarar.
Hukumar kula da lafiyar tace a shekarar 2016 yara dubu dari shida ne suka mutu sanadiyar cututtukar da ake dauka ta hanyar shakar gurbatacciyar iska , bugu da kari wani sabon rahoton hukumar lafiyar kan gurbatacciyar iska da kuma lafiyar yara ya lura cewa gurbatacciyar iskar tafi samuwa ne a tsakankanin gidaje da kuma wajen gidajen kasashen marasa abun hannu da kuma matsakaita. Binciken har ila yau yace muddin mace mai juna biyu ta kasance cikin yanayin gurbatacciyar iska, akwai yiwuwar ta haifi jaririn da bai kosa ba.
Wani dalili kuma da yasa yara suka fi fuskantar barazanar gurbatacciyar iska shine garkuwan jikinsu ba kamar na manya bane
Daga matakan daza a dauka don rage barazanar da gurbatacciyar iska ke yi wa lafiyar yara, akwai samar da makarantu da filayen wasanni masu tazara daga manyan ababen da suke haifar da gurbacewar iska da suka hada da tituna da ake hada hadar ababan hawa, masana’antu da kuma tashoshin samar da makamashi.
Saurari Cikakken rahoton Abdulwahab Mohammed:
Facebook Forum