Makon jiya, gwamnatin Obama ta zargi gwamnatin Rasha a hukumance kan sace bayanan internet na wasu cibiyoyi a Amurka da zummar yin tasiri a zaben Shugaban kasa da ke tafe, kodayake 'yansanda ba su ce wanda aka kama din na da nasaba da sace bayanan zaben ba.
Ba tare da yin cikakken bayani ba, mai magana da yawun 'yansandan Czeck David Schon ya ce makasudin gudanar da binciken shi ne kama dan Rasha din, kuma an yi nasara.
Wani bayanin da aka buga a dandalin 'yansanda na kafar internet na cewa an tsare wanda ake zargin a wani otel a birnin Prague. ‘Yansanda sun ce ya zube kasa yayin da aka zo kama shi don haka sai da aka yi masa jinyar gaggawa kafin daga bisani aka kai shi asibiti.
Bayanin ya ce kotun kasar ta Czeck ce zata yanke shawara kan ko za’a tasa keyarsa zuwa Amurka ko a'a, kodayake ba a tsaida lokaci ba ma.
To saidai Shugaban Rasha Vladimir Putin ya karyata zargin cewa da hannun Rasha a cikin lamarin.