Fico ya bayyana cewa, akwai yiwuwar samun babbar gamayyar sababbin membobin a Majalisar kasan mai zuwa, wanda yace hakan na nufin yana da babban aikin hadakar gwamnatin hadin gwiwa.
Kuri’un jin ra’ayin ra’ayoyin da gidan Talbijin din kasar Markiza ya tattaro, sun nuna cewa jam’iyyar Smer na da akalla kaso 27.3 na kuri’un da aka kada, wanda hakan wata bazata ne kasa da yadda aka zata a farko.
Gwamnatin Fico mai ra’ayin ‘yan mazan jiya tare yin adawa da shigar baki ‘yan gudun hijira cikin kasarsa, na iya ganin tutsun kuri’a tare da yiwuwar wasu masu ra’ayin mazan jiyan na iya kokarin kafa sabuwar gwamnatin da zata iya samun cikakken goyon bayan Majalisar.