Mazauna sansanin 'yan gudun hijira na wadanda su ka rasa muhallansu a Sudan Ta Kudu, sun ce sun yi matukar jin takaicin yadda aka katse ziyarar da Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Nikki Harley ta kai wurin ranar Laraba. Da damansu na zargin wata kungiyar agaji ta 'yan Faransa da ke tafi da sannanin, da hana Harley ganin irin mawuyancin yanayin da su ke ciki.
Jami'ai sun fadi a wancan lokacin cewa an katse ziyarar da Harley ta kai Sansanin ne saboda dalilai na tsaro, ganin yadda ake wata kazamar zanga-zanga kan Shugaba Salva Kiir. Katse wannan ziyarar dai ya janyo wata zanga-zangar kuma tsakanin mazauna sansanin, wadanda su ka kuhula saboda rashin ganin Jakadiya Harley.
Tut Albino, Mataimakin Shugaban daya bangaren sansanin, ya gaya ma sashin Sudan Ta Kudu na Muryar Amurka cewa, mazauna sansanin sun fusata ne saboda kungiyar agajin ta 'yan Faransa mai suna ACTED, wadda ke gudanar da sansanin; ita ta hana ganawar.
Facebook Forum