Gwamnatin yankin Catalonia ta fadi da safiyar yau Litini cewa sakamakon da aka soma samu na kuri'ar raba gardamar da aka gudanar ya nuna cewa kashi 90% na wadanda su ka kada kuri'ar jiya Lahadi na bukatar gwamnatin ta ayyana 'yancin kai daga Spain.
Mai magana da yawun gwamnatin yankin na Catalonia Jordi Turull ya ce kuri'u sama da miliyan 2 daga cikin kuri'u miliyan 2.26 na goyon bayan 'yancin kai ne.
Shugaban Catalonia Carles Puigdemont ya fadi gabanin nan cewa zai yi gaban kansa wajen ayyana 'yancin kai daga Spain muddun masu kada kuri'a sama da kashi 50% su ka zabi ballewa.
To saidai gwamnatin Spain, ta ki sam-sam.
Jami'ai daga yankin na Catalonia sun ce mutane sama da 800 sun ji raunuka bayan da 'yan sanda su ka nemi hana mutane kada kuri'a. Kotun Kundin Tsarin Mulkin Spain ta dage dokar da Majalisar Dokokin Yankin ta kafa ta gudanar da zaben, amma duk da haka aka gudanar da shi.
Facebook Forum