Kasashen sun hada da Argentina, Brazil, Ingila, Faransa, Sifaniya da Belgium.
Har ila yau akwai Portugal, Jamus, Netherlands, Croatia, Denmark, Mexico da kuma kasar Amurka.
Sauran su ne, kasar Senegal, da Wales, Poland, da Austaraliya, Japan, Morocco, Switzerland, Ghana da kuma Hadaddiyar Kasar Koreya.
Sai kasar Kamaru, Sabiya, Canada, Costa Rica, Tunisiya, Saudi Arabia, Iran, da Kasar Ecaudor da masu masaukin baki kasar Qatar.
Har yanzu dai, kan batun shirin wasan kwallon kafa na Duniya na shekara ta 2022, Kocin Ingila, Gareth South Gate, ya gargadi , Marcus Rashford, da kuma Jadon Sancho, cewa akwai yiwuwar sunansu ba zai kasance cikin tawagar din Ingila ba, na gasar cin kofin duniya ta 2022.
Ya shaida musu cewa, suka ra zagewa sosai muddin suna son su kasance cikin ‘yan wasan da za su taka leda wa kasar Ingila a gasar kwallon kafa na duniya da za a gudanar a kasar ta Qatar.
Sai kuma batun abin kunyan da ya faru a hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA, inda tsohon shugaban, Michel Platini, ya bayyana cewa, lalle kan an shirya magudi, a gasar kwallon kafa ta Duniya a shekarar, 1998, inda ya ce ya yi katsalandan, wajen tsara yadda tima-timai za su kara da juna, ta hanyar tabbatar da cewa, kasar Faransa da kasar Barazil sun hadu a wasan karshe.
Faransa wacce ita ce ta dauki bakoncin gasar, sun fafata da kasar Barazil, wanda kuma daga karshe Faransa ce ta yi nasarar lashe kofin.
Ahalin da ake ciki, Michel Platini, yana fuskantar sharia’a tare da tsohon shugaban hukumar FIFA, Sepp Blatter, kan batun rashawa da cin hanci.
Saurari cikakken rahoton Abdulwahab Muhammad daga Bauchi: