Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yan Taliban Sun Aika Sakon Gaisuwar Sallah Ga Sojojin Afghanistan


Mayakan Taliban na Sauraran Jawabin Shugabansu a yankin Herat, Afghanistan, May 27 2016.
Mayakan Taliban na Sauraran Jawabin Shugabansu a yankin Herat, Afghanistan, May 27 2016.

Ko wannan shirin na tsagaita wuta tsakanin gwamnatin Afghanistan da na mayakan Taliban zai dore?

Bangarori biyu da basa ga maciji da juna a Afghanistan sun dakatar da fadace-fadace a filin yaki na wucin gadi a karo na farko cikin shekaru 18 bayan yarjejeniyar tsagaita wuta da Taliban ya fara aiki a yau Juma’a.

Tuni gwamnatin Afghanistan ta dakatar da shirin ta na kai hare hare na tsawon mako guda wanda ya fara a ranar Talata da ta gabata domin karfafawa Yan kungiyar Taliban gwiwa da su zauna a teburin neman daidaitawa wacce zata kawo karshen mummunan yakin da ake a kasar.

Kungiyar da ke kai hare haren tayi alkawarin baza ta kai hari kan jami’an tsaron Afghanistan ba a cikin kwanaki uku na bikin karamar Sallah da za’a fara a yau wanda ya kawo karshen watan azumin Ramadan.

Shafukan sada zumunta na yanar gizo dake goyon bayan Taliban sun nuna maharan kungiyar na mika gaisuwar sallah ga jami’an sojin Afghanistan a yankuna da dama na kasar.

A wani dan gajeran jawabi da yayi wa kasar ta talabijin jim kadan bayan gama sallar idi, shugaban kasar Afghanistan Ashraf Ghani ya bada sanarwar duka bangarorin biyu sun aminta da tsagaita wuta da za’a fara tsakar daren jiya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG