A karamar hukumar mulkin Illela dake iyaka da birnin N'Konnin Jamhuriyar Nijar ‘yan bindiga kuma masu garkuwa da mutane ne suka zafafa kan hare-hare a baya-bayan nan, inda suka wuce da mutane da suka kai 20 a kasuwar ruwa.
Ko da yake, an sako wadansu daga cikin su, biyo bayan sun dauke wani mutun a garin na Illela, inda suka kashe mutane 2 a Tsangalandame da 2 a Tabkin Taramna, kamar yanda Honorable Injiniya Salihu Aliyu Ciaman na karamar hukumar mulkin Illela ya tabbatar mana.
A cikin wannan lamarin, hukumomin wannan yankin sun yi nasara cafke wadansu da ke kwarmatawa ‘yan bindigar bayanai kan inda gidajen mutane suke, a cewar Honorable Injiniya Salihu Aliyu Ciaman na Illela Local Govment.
Jama'ar wannan karamar hukumar na ci gaba da yin kira ga mahukunta na Najeriya da su kawo musu dauki ganin cewa, har da rana tsaka, ‘yan ta'addar kan dauki kasadar abkawa wadanda ba su san hawa ba, balle sauka.
Saurari rahoto cikin sauti daga Harouna Mamane Bako: