Sabon salon da ‘yan bindiga suka bullo da shi a jihar Zamfarar Nigeria wanda kuma ke kokarin bazuwa zuwa jihohin Sokoto da Katsina har ma da yankin Maradi a jamhuriayr Niger na daga cikin mahimman batutuwan da ministocin tsaron Nigeria da Niger suka tattauna a yayin ziyara da Ministan tsaron Nigeria Mansur Dan Aliyak ai Jamhuriyar Niger.
Ziyarar ta kuma bashi damar ganawa da shugaban kasarMahamadou Issoufou.
Minista Mansur Dan Ali ya ce « fadan da akan samu a jihohin Zamfara, Katsina da Sokoto kan hadasa kalubala, saboda yawancin lokaci idan an koro ‘yan ta’adda daga wannan kasa sai su koma waccan. Mun zauna mun gano yadda yakamata mu yi maganinsu »
Farfadowar aiyukan boko haram a yankin arewa maso gabashin Nigeria a wani lokacin da aka yi zaton an murkushe wannan kungiya kwata kwata, wani bangare ne na makasudin wannan rangadi da ministan tsaron Nigeria yak ai, domin matsalar ta shafi dukkan kasashen yankin tafkin Chadin.
Mansur Dan Ali yace fadan Boko Haram ba abu ba ne da za’a ce ana gama dashi rana daya. Yana cikin abubuwan da muka zo muka tattauna akan yadda za’a kara yunkurawa, domin ganin an yi maganinsu. Haka yace zai kai ziyara Kamaru, da Chadi domin ganin yadda za’a kara kaimi akan wadann nan abubuwa saboda kowace ya kamata ta kara kaimi da karfi »
Gwamnatin jamhuriyar Niger ta jaddada aniyar baiwa hukumomin Nigeria hadin kai a ci gaba da daukar matakan dakile dukkan wani yunkurin ‘yan bindigar da ke neman mayarda Niger mafaka abinda ya sa kasashen biyu baiwa junansu izinin fatattakar masu tayar da kayar baya ba tare da yin la’akari da kan iyaka ba.
Ministan tsaron kasar Niger Kalla Moutari da takwaran aikinsa na Nigeria Mansur Dan Ali da kwamandan rundunar hadin gwuiwar kasashen yankin tafkin Chadi ya raka, sun rattaba hannu akan wata yarjejeniyar hada karfi da karfe da zummar tunkarar kowane irin kalubalen tsaro dake yi wa zaman lafiyar al’umomin wadanan kasashe biyu da ake yiwa kirarin Hassan da Useni, barazana.
A saurari rahoton Souley Barma
Facebook Forum