Tun da sanyin safiyar yau ne dai masu zanga zanga aksari matasa suka yi
dafifi a harabar shiga filin wasa na kasa da ke Surulere domin amsa kiran jagoran juyin juya halin, Omoyele Sowere, da yanzu haka yake tsare a Abuja.
Sai dai duk da sammakonsu, sun tarar da tarin 'yan sanda suna jiransu, inda kuma suka umarce su, su watse, amma masu zanga zangar suka bijirewa kiran.
Wani mai zanga zangar ya shedawa manema labarai cewa, sanin kowa ne lokacin da aka yi juyin juya hali a Masar, shugaba Buhari kafin ya hau ragamar mulki, ya ce wannan shi ne hanyar kawar da gwamnati mara adalci, me ya sa kuma yanzu domin yana mulki yake adawa da wannan hanyan?
A bangarensu dai 'yan sanda sun ce masu zanga zangar ba su nemi izini ba, don haka suka yi amfani da barkonon tsohuwa domin tarwatsa su.
Yanzu dai an wasta taron, amma su masu zanga zangar sun ce za su sake komawa.
Wasu rahotanni sun yi nuni da cewa, an yi makamanciyar wannan zanga zanga a wasu yankunan Najeriyar, inda har ake zargin 'yan sandan da yin amfani da karfin da ya wuce kima wajen tarwatsa masu boren neman sauyin.
Ga cikakken rahoton daga wakilin Muryar Amurka Babangida Jibrin daga Legas.
Facebook Forum