Hukumomin ‘yan sandan jihar Ogun sun ayyana neman mawakin nan mai yawan janyo cece-kuce, Habeeb Olalomi, da aka fi sani da Portable ruwa a jallo, saboda zargin kai mummunan hari akan jami’an gwamnatin dake gudanar da ayyukansu bisa doran doka.
Ayyanawar na kunshe ne a cikin jaridar rundunar ‘yan sandan da aka wallafa a daren jiya Litinin, wacce kakakin rundunar ta jihar Ogun, Omolola Odutola ya yada.
A cewarta, harin ya faru ne a ranar 5 ga watan Febrairun 2025, da misalin karfe 10 na safe sa’ilin da jami’an shiyar Ota na ma’aikatar tsara birane ta jihar Ogun; Onabanjo Abidemi da Raymond Lateef da Ridwan Oyero Akinlesi ke tsaka da gudanar da aikinsu na tursasa bin dokar gine-gine a yankunan Oke-Osa da Tigbo Ilu Ota.
Dandalin Mu Tattauna