Ana ci gaba da musayar yawu tsakanin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna da almajiran Shaikh Ibrahim El-Zakzaky wanda ake yiwa shari’a.
Yayinda ‘yan sandan ke cewa taho mu gama da suka yi da ‘yan darikar Shiya ta yi sanadin salwantar ran wani jami’insu tare da jikata wasu jami’an su kuwa ‘yan Shiyan cewa suke basu kashe kowa ba.
Mai magana da yawun ‘yan sandan Mukhtar Aliyu ya yiwa manema labarai karin bayani cewa jiya Alhamis da misalin karfe 11 zuwa 12 bayan an dage shari’ar Shaikh Ibrahim El-Zakzaky, almajiransa suka fito suka tare hanya suna cewa ba wanda zai wuce.
Mukhtari Aliyu y ace ba karamin laifi ba ne a tare mutum a hana shi tafiya inda za shi. Suna kokarin ganin cewa an bar mutane sun tafi inda zasu, sai mabiya Shiyan suka jefi dan sandan su suka kuma yi amfani da wuka suka caccackeshi. Koda suka isa asibiti an tabbatar masu cewa yam mutu.
A cikin hargitsin ‘yan sanda sun kama ‘yan Shiya 11, suna zargin su da laifin suna da hannu a kisan jami’insu da kuma raunata wasu.
To sai dai kakakin almajiran Shaikh Ibrahim El-Zakzaky Malam Abdulmummuni Giwa ya ce mabiya kungiyar masu neman zaman lafiya ne saboda haka su basu kashe kowa ba. Amma su sun dauki matsayinsu ne na cewa basu yadda a ci gaba da tsare jagoransu..
Ya ce abun da suke fada ke nan akan titi suna tafiya. Zargi ne kawai ‘yan sanda keyi domin babu wani dalilin da zai sa su kashe wani saboda wai, ba tsarinsu ba ne.
Shekaru uku ke nan ana tsare da madugunsu. Ya ce amma su zasu iya cewa akalla ‘yan sanda sun kashe masu mutum sama da 27 a Kaduna kawai. Sannan sun kama masu mutum 11 kuma suna zargin cewa akwai gawarwakin ‘yan uwansu ‘yan Shiya a hannun ‘yan sandan.
Duk da bayanin kakakin ‘yan Shiya din bai hana ‘yan sanda kawo hujjojinsu na cewa ‘yan Shiyan ne suka kashe masu jami’i. Mukhtari Aliyu y ace duk abun da ya faru a gaban jama’a aka yi kuma akwai hotuna da bidiyo. Y ace da sukan sanya kayan dake nunasu amma a wannan karon sai suka bace cikin jama’a inda suka samu suka yi anfani da manyan duwatsu da suka jefi dan sandan tare da fasa motocin ‘yan sanda. Amma zasu ci gaba da bincike su gurfanar da duk wadanda suke da hannu a lamarin.
Wani mutum mai suna Muhammad Gambo daya daga cikin mutanen da hargitsin ya rutsa dasu y ace abun ba karamin tsanani ya yi ba. Yace da so samu ne a saki malaminsu domin a samu zaman lafiya. Shi ko Awal Ibrahim y ace rigimar ta jiya ta bashi tsoro domin bai taba ganin irinta ba. Sai dai y ace sakin malamin zai kara dagula sha’ani, za’a shiga wata sabuwar rigima. Kamata ya yi a cigaba da rikeshi har gwamnati ta san abun da zata yi.
Alkalin da ya kamata ya saurari karar bai zauna ba saboda bai ji dadi ba kamar yadda lauyan Shaikh din ya tabbatar. An tsaida ranar 11 ga watan gobe su koma kotun.
A saurari rahoton Isa Lawal Ikara da karin bayani
Facebook Forum