Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle, ya ba da umarnin bude hanyoyin sadarwa da aka rufe a yankin Gusau.
Umarnin zai fara aiki a ranar Juma’a a cewar mai ba gwamnan shawara kan sha’anin yada labarai Zailani Bappa.
“Maido da hanyoyi sadarwar ya zama dole saboda dumbin nasarorin da aka samu a yakin da ake yi da ‘yan bindiga a jihar, hakan kuma wani mataki ne na saukaka wahalhalun da bangarorin jama’a da na masu zaman kansu suka shiga.” In ji Bappa.
Gwamnatin jihar ta Zamfara ta ce “babu shakka matakin rufe hanyoyin sadarwar ya dagula al’amuran gungun ‘yan ta’adda, abin da ya sa jami’an tsaro suka samu nasara.”
“Gwamna Matawalle ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da sa ido kan abubuwan da ke wakana, sannan za ta sanar da matakai na gaba.” Sanarwar ta kara da cewa.
A farkon watan Satumbar da ya shude hukumomin jihar suka sanar da matakin rufe hanyoyinn sadarwar na wayoyin tare da hadin gwiwar hukumar da ke kula da kamfanonin sadarwa ta NCC a Najeriya.
An dauki matakin ne don a kassara ayyukan ‘yan fashin dajin da suka addabi jihar ta Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriyar.