Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Sanda a Nijar Sun Cafke Wasu Gaggan ‘Yan Fashi


Hukumar ‘yan Sanda a Jamhuriyar Nijer ta cafke wasu gaggan ‘yan fashi da makami da suka addabi jama’a a tsakanin kasar ta Nijer da makwaftanta, inda suka hallaka mutane da dama tare da karbe dimbin dukiyoyi.

Yawaitar korafe-korafen jama’a da kashe-kashen da aka fuskanta a tsakanin watannin Fabrairu, Maris da Afrliun da suka gabata a birnin Yamai da wasu jihohin Nijer ne ya sa hukumar ‘yan Sandan farin kaya ta kaddamar da binciken, inda a karshensa dubun wasu ‘yan Fashi kimanin su 14 ta cika, wadanda suka hada da ‘yan Nijer da ‘yan wata kasa makwafciyar ta, da ba a bayyana sunanta ba.

An Kama 'Yan Fashi da Makami A Niger
An Kama 'Yan Fashi da Makami A Niger

Alkali mai kare muradun gwamnati da alkalin alkalai da mukarrabansu sun ziyarci ofishin ‘yan Sandan PJ domin jinjinawa wadanan jami’ai.

‘Yan Fashin wadanda galibinsu matasa ne an gabatarda su ga manema labarai a farfajiyar ofishin ‘yan Sandan farin kaya, inda a aka baje bindigogi da harsasan da suke amfani da su wajen aikata laifin.

A cikin ‘yan fashin har da wani matashi dan kimanin shekaru 16 da haifuwa, wanda shi ma ke dauke da bindiga, inji Ousman Barglo mataimakin Alkalin Alkalai.

An Kama 'Yan Fashi da Makami A Niger
An Kama 'Yan Fashi da Makami A Niger

Hukumar ‘yan Sanda ta jaddada aniyar ci gaba da farautar barayi da ‘yan fashi da dukkan wasu ‘yan takifen dake hanawa jama’a sakewa, musaman a birane inda amfani da makami ta irin wadanan hanyoyi ke kokarin samun gindin zama.

Saurari Karin bayani cikin sauti daga Souley Moumouni Barma.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG