Hukumomin Jamhuriyar Nijar sun fitar da sanarwar rasuwar ministan kwadagon kasar Ben Omar.
Omar ya rasu ne a ranar Lahadi a babban asibitin kasar da ake kira Hopital General de Reference da ke birnin Yamai inda ya shafe kwanaki yana jinya.
Kafin a ba shi mukamin ministan kwadago, Mohamed Ben Omar ya rike mukamin ministan ilimi daga shekarar 2016 zuwa 2017.
Sannan ya kuma rike mukamin mataimaki na 5 na kakakin majalisar dokokin Nijar a wa’adin mulkin farko na shugaba Issouhou Mahamadou.
Fitaccen dan siyasa ne da ya taka rawa a zamanin Jamhuriya ta 4 a karkashin Gen. Ibrahim Ba’are Mainassara musamman wajen kafa jam’iyyar RDP Jama’a.
Haka kuma Ben Omar ya rike mukamin ministan sadarwa kakakin gwamnati a zamanin shugaba Tanja Mamadou inda ya yi tsayin daka wajen ganin Tanja ya zarce akan karaga bayan shudewar wa’adinsa na 2 a karshen shekarar 2009.
Rikicin shugabancin da ya kunno kai a jam’iyyar RDP jama’a ya sa Mohamed Ben Omar da magoya bayansa ficewa daga wannan jam’iya don kafa PSD Basira a shekarar 2015 wato watanni kadan kafin zabukan shekarar 2016 kuma duk da haka wannan jam’iyya ta samu kujerun wakilci a majalisar dokokin kasa.
Shugaban kasar Nijar Issouhou Mahamadou a shafinsa na Twitter ya bayyana alhini a game da abin da ya kira babban rashi.
Dan kimanin shekaru 55 da haifuwa marigayi Mohamed Ben malamin makaranta ne da ya lakanci aikin koyarwa a makarantun share fagen shiga jami’a.
A wannan Litinin ne ake sa ran za yi jana’izarsa karkashin jagorancin shugaba Issouhou Mahamadou kafin a yi masa rakiya zuwa makwancinsa na karshe.
Saurari wannan rahoton a sauti.
Facebook Forum