WASHINGTON, DC —
Mahamadoul Kafi Djibrilla daga Janhuriyar Nijar, mai fashin baki ne akan harkokin wasanni da rubutu, yayi tsokaci.
“Kamaru, kafin su je gasar dama suna da matsalar kudi. To idan zaka je kwallo, kuma hankali bai kwanta ba, dole a samu matsala”, a cewar Mr. Djibrilla.
Game da wasan Ghana kuwa “sun saba cin Amurka, sai sukayi kwallo wanda bai kamata ba, sun saka zuciya, amma basu yi nasara ba. Najeriya kuwa, Iran ya kamata a ce ta ci, amma sai sukayi kunnen doki.”
Mr. Mahamadoul Kafi yace baza’a iya tantance irin tasirin da kungiyoyin kasashen Afirka zasu yi ba, sai Aljeriya ta kammala wasanta da Beljom.