Yan Najeriya da suka rako shugaba Muhammadu Buhari a ziyarar sa a Amurka sun bayyana raayoyin su game da ziyarar da Shugaban ya kai Amurka.
Aliyu Mustafan Sokoto ya zanta da wasu daga cikin su, kuma ya fara ne da Adamu Aliyu na hannun damar shugaba Buharin kuma tsohon dan majilisar wakilai na Najeriya.
Aliyu ya fara tambayar sa ne ko me suke jin game da batun cewa Amurka zata gabatar da batun auren jinsi guda ga shugaba Buhari? Ga kuma amsar da ya bayar kamar haka.
‘’Waiyazu billa na farko dai Najeriya Musulmai ne mu da kiristoci addinan namu gaba daya basu yadda da wannan ba, addinan mu gaba daya sunyi ALLAH waddarai da wannan abu, kuma na tabbatar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari koda wannan maganar zata taso na tabbatar zaiyi ALLAH Waddarai da ita domin Najeriya da yan Najeriya basu amince da wannan ba kuma yan Najeriya ne suka zabe shi.
To kasan Amurkawa tunanen su ya banbanta dana yan Najeriya wanda yasa har ake cewa wasu kusoshin gwamnati zasu tuntubi shi shugaba Buhari da wannan batu dukkan raayoyin da ake nunawa shine ana nuna cewa raayin yan Najeriya basa so, to kuma akwai harkan diflomasiyya a cikin tattaunawan shugabannin din ta yaya zasu tinkari wannan Kenan ?
‘’To Magana dai it ace kowa da kasar sa kowa da yadda kasar sa take, Muhammadu Buhari shugaban Najeriya ne da yadda kasar Najeriya take, shi kuma shugaba Barak Obama shugaban Amurka ne akwai yadda Amurkawa suke nasu tabiaar su da abubuwan su, wannan abu muna ALLAH waddarai dashi kuma na tabbatar idan aka matsa idan aka matsa shugaban Najeriya zaiyi ALLAH waddarai da wannan batu domin Najeriya da yake mulkin ta, yake jagorancin ta bata yadda dashi ba addinan mu duka basu yadda dashi bas abo da haka na tabbatar kome diflomasiyya ba yadda za ayi mu yadda da wannan abu.
Dama a cikin tawagar na shugaba Buhari akwai yan kasuwa suko ga abinda suke fata wannan ziyarar ta samar da farko dai ga Sardauna Habib.
‘’Na farko muna son muga an kara bunkasa harkokin kasuwanci tsakanin Najeriya da Amurka da kuma bada dama a samu cigaba da abubuwan da suka shafi noma da sauran ayyuka’’.
Ko akwai wasu takammamun sanaoi ko ayyuka da kuke fatan ganin an bunkasa tsakanin kasashen biyu.
‘’A to Kaman dai noma da kara bunkasa harkokin ilmi usammam ilmi na kimiyya dana fasaha’’.
To shima Alhaji Abubakar Musa shima ga abinda yace yana fata ganin wannan ziyarar ta samar .
‘’Babban abinda muke shaawa mu gani shine gyara tsarin tafiyar da gwamnati idan aka inganta hukumomi to ba shakka abubuwa zasu kyau kuma abubuwa zasu tafi dai-dai’’.
Bayan wannan akwai wani fanni da kake fatar ganin an tabo bayan wannan?
‘’To babban dai abu shine tsaro komi idan babu tsaro komi ba zai tafi dai-dai ba, amma idan aka samu tsaro sai a tabbatar da kuma an baiwa harkan ilmi muhimmanci sai kuma harkokin da suka shafi maadanai da harkar noma’’.
Ga Dai Aliyu Mustafa da bakin nasa