Sanadiyar fashewar bamabamai biyu ya jawo asarar rayukan da kuma wadanda suka jikata.
To saidai alkaluman ka iya canzawa loto loto saboda wasu da suka ji munanan raunuka kamar yadda wani jami'in hukumar dake bada agajin gaggawa ya fada.
Duk da abun da ya faru jama'ar garin sun fito sun taimaka. Haka ma 'yan kungiyoyin agaji sun fito suka taimaka.
Bangaren da abun ya faru basu yi hada hadar sallah ba. Kowa na cikin juyayin abun da ya faru.
Jami'in hukumar bada agaji yace idan mutane sun zo taimako suka ga wanda ya samu rauni to kada a yi saurin dagashi domin ana iya kara mashi rauni. A bari sai an samu wanda ya san kan lamarin, wato yana da horo akan yadda ake taimakawa wanda ya raunata.
DSP Fagge Attajiri kakakin 'yansandan jihar Gombe ya kara haske kan abun da ya faru. Yace jiya lokacin da mutane ke kokarin sayen kayan sallah sai bamabamai biyu suka tashi. Yace sun fara bincike domin gano wadan suke da hannu a lamarin.
Ga rahoton Abdulwahab Muhammad da karin bayani.