Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Janhuriyar Nijar Mazauna Jihar Neja A Najeriya Sun Bukaci Karin Lokacin Yin Rajistar Zabe

‘Yan Kasar Nijar Mazauna Jihar Nejan Najeriya Sun Bukaci Karin Lokacin Yin Rajistan Zabe
‘Yan Kasar Nijar Mazauna Jihar Nejan Najeriya Sun Bukaci Karin Lokacin Yin Rajistan Zabe

Daruruwan 'yan kasar Jamhuriyar Nijar da ke zaune a Najeriya na ci gaba da yin tururuwa zuwa yin rujistar zabe da hukumar zaben kasar ta Nijar wato SENI ke yi.

NIGER, NIGERIA - A Jihar Neja kimanin ‘yan kasar Nijar 5000 ne ake sa ran za su yi rijistar zaben da zata basu damar kada kuri’a a Najeriya a lokacin gudanar da zaben a can kasar Nijar.

Sai dai ‘yan Nijar din da muka samu suna bin layin rijistar a birnin Minna sun ce lokacin da aka dibar masu ya yi kadan, kamar yadda shi ma shugaban kungiyar ‘yan kasar ta Nijar mazauna Jihar Neja, Alhaji Dalladi Ali, ya ce.

‘Yan Kasar Nijar Mazauna Jihar Nejan Najeriya Sun Bukaci Karin Lokacin Yin Rajistan Zabe
‘Yan Kasar Nijar Mazauna Jihar Nejan Najeriya Sun Bukaci Karin Lokacin Yin Rajistan Zabe

Babban jami'in hukumar zaben ta kasar Nijar dake aikin rijistar a jihar Neja Abdu Amadu Ibrahim ya ce lokacin da aka dibar masu zai ishesu su kammala aikin rijistar.

Bayanai dai sun nuna cewa idan ba a samu mutane 2000 ba a wannan rijista to ‘yan Nijar dake Jihar Neja za su tafi Abuja ne domin kada kuri’a a lokacin da za a gudanar da zaben.

Saurari cikakken rahoto daga Mustapha Nasiru Batsari:

‘Yan Kasar Nijar Mazauna Jihar Nejan Najeriya Sun Bukaci Karin Lokacin Yin Rajistan Zabe.MP3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:05 0:00

XS
SM
MD
LG