Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan jam'iyar Republican sun daina tattaunawa


Shugaban Amurka Barack Obama
Shugaban Amurka Barack Obama

Shugaban Amurka Barack Obama ya bayyana takaicin cewa, jiga-jigan jam’iyar hamayya ta Republican a majalisar wakilai sun yi watsi da tattaunawar da ake yi kan batun daga yawan kudin da Amurka zata iya rantowa duk da tayin da shugaban kasar yayi na abinda ya bayyana a matsayin sassaucin gaske.

Shugaban Amurka Barack Obama ya bayyana takaicin cewa, jiga-jigan jam’iyar hamayya ta Republican a majalisar wakilai sun yi watsi da tattaunawar da ake yi kan batun daga yawan kudin da Amurka zata iya rantowa duk da tayin da shugaban kasar yayi na abinda ya bayyana a matsayin sassaucin gaske. Mr. Obama ya bayyana jiya jumma’a cewa, ya kasa fahimtar dalilin da zai sa John Boehner zai yi watsi da irin wannan yarjejeniya. Shugaba Obama yace yanzu lokaci ya kure masu. Ya bayyana cewa, ya gayyaci jiga jiga jam’iyun biyu domin tattaunawa yau asabar a fadar White House. Shugaban kasar yace yana son ‘yan majalisar sun bayyana mashi yadda kasar zata iya biyan basukan dake kanta idan kudin kasar ya kare ranar 2 ga watan Agusta.

Mr. Obama yace ya yi tayin rage kudin da ake kashewa kan ayyukan kyautata rayuwar al’umma. Ya kuma shawarta kara kudin haraji fiye da abinda ‘yan majalisar dattijan dake tattaunawar da ta kunshi dukan jam’iyun kadan kawai. Bisa ga cewarshi, kusoshin jam’iyar Democrats basu amince da yarjejeniyar ba, sai dai a shirye suke su tattaunawa. Bisa ga cewarshi, idan ‘yan jam’iyar Republicans suka ki taimakawa wajen cimma matsaya, za a dora masu alhakin duk wani halin da za a shiga idan gwamnati ta gaza biyan dala miliyan saba’in da take kashewa kowanne wata.

Jim kadan bayan bayanin shugaba Obama, Boehner ya maida martani da cewa, tayin da shugaba Obama yayi, ya hada da karawa mutanen da ake bukata su zuba jari domin zaburar da tattalin arzikin kasar da samar da ayyukan yi haraji. Boehner yace zai hada hannu da ‘yan majalisa daga jam’iyun biyu makon nan wajen shata hanyar shawo kan lamarin, bisa ga cewarshi, ya hakikanta cewa, Amurka ba zata gaza biyan basukan da ake binta ba. Shugaba Obama yace ba zai taba amincewa da daukar kwarya-kwaryar matakin cike gibin kasafin kudin ba, yace zai bukaci a kalla a amince da ranto kudin da zai kai kasar zuwa karshen wa’adin shugaban kasar na shekara ta dubu biyu da goma sha uku

XS
SM
MD
LG