Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu 'Yan Gudun Hijirar Burundi Na Jin Tsoron Komawa Kasar


'Yan gudun hijirar kasar Burundi dake wasu kasashe sun ce suna tsoron kisa, da gana azaba daga dakarun gwamnatin kasar idan suka koma.

‘Yan gudun hijirar kasar Burundi sun ce ba su gamsu da matakan tsaron kasarsu ba da har za su koma, duk da kiraye-kirayen da shugabannin Burundi da wasu na kasashen Afrika ta tsakiya suka yi akan cewa su koma.

Wasu ‘yan gudun hijira da suka yi magana da muryar Amurka sun ce suna gudun fushin gwamnatin kasar idan suka koma Burundi, inda shugaba Pierre Nkurunziza ke cigaba da kasancewa akan karagar mulki bayan da ya bijirewa kiraye-kiraye daga kasar da kuma kasashen waje akan sake tsayawa takara karo na uku a shekarar 2015.

Jacqueline Nduwayezu, wata tsohuwar malamar makarantar sakandare, na daya daga cikin ‘yan gudun hijirar dake sansanin ‘yan gudun hijirar Mahama a gabashin Rwanda da ‘yayanta guda shidda.

Nduwayezu ta fadawa wani wakilin Muryar Amurka da ya kai ziyara sansanin kwanan nan cewa “muna nan ne saboda babu tsaro a kasar mu. Ta kara da cewa ba don jin dadi muka yi tafiya mai nisan gaske, muka bar gidajenmu da kasarmu ba amma saboda barazanar da aka yi mana. An kashe mutane, kuma har yanzu ana kan kashe su a binnesu a ramuka ko a jefa su koguna.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG