A Jamhuriyar Nijar, wasu matasa ‘yan gudun hijiran Sudan su kimanin 150 sun fara zaman dirshan na sai yadda hali ya yi.
'Yan gudun hijiran dai na zargin reshen hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da ‘yan gudun hijira wato UNHCR da saba alkawari akan batun samar musu mafaka a kasashen Turai, lamarin da hukumar ta musanta.
Matasan sun ce sun tsinci kansu a Nijar ne bayan da hukumar ta kwaso su daga Libya akan hanyarsu ta zuwa Turai a shekarar 2017.
Shekaru biyu bayan wannan mataki, ‘yan gudun hijirar na ganin an saba alkawarin da aka yi musu na samar masu mafaka a nahiyar Turai.
Wata wakiliyar hukumar a Nijer, Alexandra Morelli ta mayar da martini a kan batun.
Ta ce, “Rikicin kasar ta Libya ya sa suka bukaci a mayar dasu inda za su samu kwanciyar hankali, dalilin da ya sa kasar Nijer ta amince ta basu mafaka kenan, amma su a tunaninsu UNHCR zata kaisu Turai sai dai wannan hukumar ba kamfanin jigila ba ce ba.”
Mista Morelli ta kuma bayyana cewa hukumar HCR ta yanke hukuncin basu tallafin kudade a kowane wata, da kuma masauki har tsawon watanni uku amma ‘yan gudun hijiran suka yi watsi da tallafin.
A wani bangaren kuma, wasu ‘yan gudun hijirar Afrika ta tsakiya da Liberia da kuma Kamaru suma sun kafa sansanoni a harabar reshen hukumar ta UNCHR, saboda abin da suka kira rikon sakainar kashin da ake yiwa halin kuncin da suke ciki.
Baya ga ‘yan kasar Sudan da Eritrea da kuma Jamhuriyar Afirka ta tsakiya, Nijer na karbar bakuncin daruruwan dubban ‘yan Najeriya da ke hijira a yankunan Diffa da Maradi, sakamakon matsalar Boko Haram da kuma matsalar satar mutane a wasu jihohi kamar jihar Zamfara.
Ga karin bayani a sauti daga wakilinmu Souley Moummouni Barma.
Facebook Forum