Kungiyar likitoci ta kasa da kasa ta Doctors Without Borders, ta ce sama da ‘yan Iraqi miliyan 1 da suka tserewa rikicin kungiyar IS, na zaune a wasu sansanoni masu cunkoson jama’a masu kazanta kuma suna cikin hadarin kamuwa da cutar ta COVID-19.
Kungiyar MSF ta ce duk da cewa an samu bullar cutar a sansanonin, amma masu fita su je su yi aiki na haifar da barazanar kara kwaso cutar su shiga da ita cikin sansanonin.
Kungiyar ta ce yana da matukar wahala ga ‘yan gudun hijira su kare kansu daga yiwuwwar barkewar cutar.
Jami’an kiwon lafiya sun ce mutanen da suke da wasu larurori na rashin lafiya, kamar masu ciwon, suga, hawan jini da cuttukan zuciya, su ne suke da hadarin kamuwa da COVID-19.
A cewar Majalisar Dinkin Duniya, ’yan Iraqi miliyan 3 ne suka tserewa rikincin kungiyar IS daga 2014 har zuwa lokacin da Iraqi ta yi nasarar murkushe kungiyar ‘yan ta’addan shekaru biyu da suka gabata.
Facebook Forum