Kakakin rundunar mayakan saman Nigeria Air commodore Ibikunle Daramola, yace shirin ‘Diran Mikiya’ a Zamfara ya na samun galaba akan miyagun mutanen da suka addabi jihar.
Hare haren da sojojin ke kaiwa da jiragen yaki sun hallaka ‘yan bindiga masu dimbin yawa a wajejen kauyukan Mashema da wani wuri kilomita hudu daga kudu maso gabashin ‘Yan Mari a cikin jihar Zamfaran.
Da farko wani jirgin soji mai leken asiri ya gano wata matattarar ‘yan bindiga dadi inda jirgin yaki mai aman wuta ya barbada masu wuta ta kowane bangare. Jiragen sun yiwa bata garin kaca-kaca, babu wanda ya tsira cikinsu.
A dajin kauyen ‘Yan Kari da dajin Hayin Alhaji, jirgin yakin mayakan ya yi kicibis da wasu gungun barayin shanu sanye da bakaken kaya akan babura tare da garkunan shanun sata. Kodayake barayin sun yi kokarin arcewa amma basu ci nasara ba domin jirgin yaki ya murkushesu.
Rundunar mayakan ta sha alwashin ci gaba da kai hare haren har sai ta ga bayan muggan mutanen a jihar ta Zamfara kamar yadda babban hafsa hafsoshin mayakan saman ya shaidawa Sashen Hausa.
Air Marshal Sadique Abubakar babban hafsan hafsoshin mayakan y ace suna kai hare haren ne domin suna ganin suna da hakkin kare mutane da dukiyoyinsu. Suna son su tabbatar cewa muggan mutanen ba su yi tasiri ba ta yadda zasu tilastawa mutane gujewa daga muhallansu ba. Za su yi yaki su kare mutane za su kuma taimaka masu.
A saurari rahoton Hassan Maina Kaina
Facebook Forum